Garkuwan Cindo Ya Buge Ghali, Ramadan Ya Doke Bahagon Kanawa
Daga BBC Hausa
Garkuwan Cindo ya buge Ghali Shagon Dogon Auta a damben kofi da suka dambata a gidan wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Najeriya ranar Litinin.
Tsohon Sarkin damben gargajiya Guramada ya yi nasara a kan Ghali daga Kudu a turmi na biyu.
Sauran sakamakon wasannin da aka buga a damben matasa kuwa don lashe mota, Ramadan daga Jamus ya buge Shagon Bahagon Kanawa daga Kudu a turmin farko.
Autan Bahagon Mancha daga Jamus ya doke Gatkuwan Sama’ila daha Kudu a turmi na biyu.
Autan ‘Yar biyat ya buge Shagon Bahagon Mai Maciji daga Kudu a turnin farko.