Fiye Da Manoma 4,000 Za Su Amfana Daga Noman Rani a Kogin Watari – Gawuna

Daga Aliyu Dangida

Dantakarar kujerar Gwamnan jihar Kano a karkashin Jam’iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bada tabbacin cewar fiye da manoma 4,000 ne za su amfana daga noman rani wanda Gwamnatin Ganduje ta aiwatar daga kogin Watari.

Gawuna ya bada tabbacin hakan a yayin gabatar da jawabinsa wajen yakin neman zaben takararsa da mataimakinsa (Gawuna/Garo) ga al’umomin kananan hukumomin Bagwai da Shanono.

Yace gwamnatinsu ta samar da kadada 1,000 a kogin Watari da ke karamar hukumar Bagwai, a kokarin gwamnati na inganta noman rani tare da bunkasa samar da abinci ga al’umomin yankunan da sauran sassan jihar.

Nasiru Gawuna ya ce an fara aikin ne lokacin yana rike da mukamin kwamishina na ma’aikatar ayyukan gona a karkashin gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da niyyar samar da ayyukan yi ga dinbin al’ummomin yanki da bunkasa tattalin arziki.

Ya bukaci matasan yanki da su yi amfani da wannan dama da gwamnati ta samar a yankunansu don yi noman rani da zumar dogaro da kai tare da rage tafiye-tafiye zuwa wasu garuruwa don neman kudi.

Ya tabbatarwa al’ummomin kananan hukumomin biyu cewar idan aka zabe shi, zai dora daga inda gwamnatin Ganduje ta tsaya wajen samar da ayyukan more rayuwa masu nasaba da inganta rayuwar al’umma.

A nasa jawabin dantakarar mataimakin Gwamnan jihar Kano, Murtala Sule Garo ya godewa dandazon al’ummar kananan hukumomin Bagwai da Shanono bisa fitowa mazansu da matansu, yara da matasa domin nuna goyon bayansu ga jam’iyyar APC

Murtala Garo ya kuma shawarce su da su ci gaba da bai wa Jam’iyyar APC da ‘yan takarar ta hadin kai da goyon baya domin samun nasarar zaben 2023.

Yayin gudanar da gangamin yakin neman zaben an mika tuta ga ‘yan takara a matakai daban-daban tare da karbar daruruwan ‘yan Jam’iyyar NNPP magoya bayan tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso wanda suka canja sheka zuwa Jam’iyyar APC.

Mahangar Arewa ta ruwaito cewar makada da mawaka sun baje basirarsu a yayin gangamin yakin neman zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: