DSS Ta Kama Masu Cazar Jama’a Kafin Su Canja Musu Sababbin Kudi

Daga Mujtaba Gali

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS, ta sanar da kama wasu miyagu masu aikata laifukan sayar wa ‘yan kasar sababbin takardun kudin da gwamnati ta fitar a sassan kasar.

Wannan na cikin wata sanarwa da hukumar tsaron ta fitar ta hannun kakakinta Dr Peter Afunanya a ranar Litinin a Abuja babban birnin kasar.

Ya ce jami’an hukumar ne suka damke gungun masu aikata laifin yayin da suke tsakiyar hada-hada. Ya kuma ce, “Binciken mu ya nuna cewa wasu jami’an bankunan kasuwanci na taimaka wa masu aikata wannan zagon kasar da ake wa tattalin arziki.”

Hukumar ta gargadi al’umomin kasar da su taimaka wa jami’anta da bayanan dukkan wuraren da suka san ana yin wannan haramtaccen cinikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: