Dr. Bishir Gambo Saulawa: Yabon Gwani Ya Zama Dole
Daga Maiwada Dammallam
Na halarci zaman majalisa na ranar litinin 30/8/22 dan karrama tantancewar da Majalisa ta yi wa Dr. Bishir Gambo Saulawa a matsayin Kwamishina.
Hakika, duk wanda ya halarci wannan tantacewar zai yadda cewa Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari yayi hangen nesa wajen gayyatar Dr. Bishir Gambo shiga cikin Majalisar zartaswa ta Jihar Katsina.
Kama daga ‘yan rakiyar Dr. Bishir Gambo zuwa Majalisa don tantacewa, wadanda suka hada da mutane daga jam’iyu daban daban, zuwa irin karamci da ya samu daga y’an majalisa gaba daya, mutum zai gane an zabo mutum da yake zaune lafiya da al’umma cikin girma da arziki.
Duk wanda ya saurari jawabin mataimakin shugaban majalisa, Hon. (Engr) Shehu Dalhatu, lokacin da ya gabatar da Dr. Bishir Gambo don Majalisa ta wanke shi, da kuma lokacin da shi kan shi Dr. Bishir Gambo yake gabatar da kanshi, mutum zai yarda Hon. Bishir Gambo mutum ne da ya san abinda yake kuma yake da tarihin gwagwarmaya kan harkar gina kasa da inganta rayuwar al’umma.
Hakika, Dr. Bishir Gambo ya samu horo na musamman hannun manyan ‘yan siyasa da su kayi fice a Najeriya kuma aka dade ana damawa dasu.
Dalibi ne a gidan siyasar Marigayi Shugaban Kasa, Malam Umar Musa da gidan siyasar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Lawal Kaita. Hakan ya bashi dimbin fahintar irin rikita rikitar dake cikin siyasar Najeriya tun yana da kananan shekaru.
A yau, bana zaton akwai dan siyasar da ya amsa sunan shi a Jihar Katsina da ba ya ganin girman Dr. Bashir Gambo saboda amincin shi da kyawawan d’abi’o’in shi.
A fannin bokon zamani, Dr. Bishir Gambo ya samu horo isasshe daga fitattun jami’o’i na cikin gida Najeriya da ketare har ya kai kololuwar fannin da ya zaba don shahara.
Abin ya ba kowa sha’awa bayan ya gama gabatar da kan shi ga Majalisa, duk dan Majalisar da zai yi tsokaci, sai ya fadi “Intimidating CV din Dr. Bishir Gambo” tsokacin shi.
Ya samu gogewar siyasi irin wadda duk dan siyasa ya kamata ace ya samu. Ya faro tafiyar siyasar daga kasa, ya bi mataki mataki ya hawo sama.
Hakan ya sa ya zama dan siyasa wanda zai iya yin zarra duk gurbin da ya samu kan shi a fagen shugabanci daga dan autan mahukunta har zuwa Shugaban Kasa.
A kishin al’umma, duk wanda ya san Dr. Bishir Gambo zai yarda cewa abin duniya bai rufe mashi ido ba. Yana daga cikin ‘yan siyasar da na sani wadanda nan tana jin sunan su ya gitta cikin maganar zaluntar al’umma ba.
A dayan hannu, ni ba jiyau bane ganau ne kan irin dagewar shi ta ganin ba’a zalunci al’umma ba.
A shekarar 2021, ya gayyace ni cikin wata badakala da wani dan siyasa ya wawuri wasu kudade kusan Naira Biliyan daya, wadanda aka ware don wasu ayyuka a Jihar Katsina aka karkatar da su. Haka muka shiga, muka fita, tare da hadin guiwar wasu ‘yan majalisar tarayya sai da aka maida kudin gurbin da yakamata.
Nan gaba zan kawo cikakken labarin yadda abin ya faru, wadanda sukayi abin da wadanda suka taimaka aka rusa abin. A biyo ni bashi.
Akan haka, bana haufin al’umma za su samu adalci da ribar abinda Maigirma Gwamna Masari ya hanga ya zabi Dr. Bishir Gambo a matsayin Kwamishina dan al’umma su amfana.
Ina masa fatan alkhairi da kuma fatan Allah Ya kama mashi wajen sauke wannan nauyin da Allah Ya dora mashi.
A karshe, ina mika godiya ta musamman ga Mataimakin Kakakin Majalisa, Rt. Hon. (Engr) Shehu Dalhatu wanda ya jagoranci zaman kuma ya mutunta ni ta hanyar yi man barka da zuwa zauren majalisar bayan ya hange ni cikin dimbin tawagar da suka raka Dr. Bishir Gambo wajen tantancewa. Ina godiya da mutuntawa Rt. Hon. Sir.