Dan Takarar Gwamnan Jihar Yobe A NNPP Ya Yi Alkawarin Inganta Ilimi, Noma, lafiya da Sauran su

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Dan takarar gwamnan jihar Yobe a karkashin jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP), Mallam Garba Umar, ya jaddada kudirin jam’iyyarsa na inganta harkokin  Ilimi, noma, kiwon lafiya, da fannin gidaje da kuma jin dadin ma’aikatan jihar da sauran su, idan an zabe su a zaben da ke tafe na 2023. 

Malam Garba Umar ya bayyana haka ne a ranar yayin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar da ke Damaturu kan shirye-shiryensu na karbar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabi’u Musa Kwankoso a jihar.

A cewar, sa yana bada tabbaci ga al’ummar Yobe cewar, matukar suka hau mulki to kuwa gwamnatin su baza ta taba lamunta da duk wani aikin da ba shi da nagarta sabanin gwamnatin yanzu da ta ke gudanar da ayyukan gidajen da tun ma ba a shiga ba sun fara lalacewa saboda tsananin rashin Ingancin aiki. 

Dangane da ziyarar dan takarar su na shugaban kasa Dr Rabi’u Musa Kwankwaso a jihar su ta Yobe kuwa, a cewar sa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsu zai ziyarci yankunan Yobe ta Arewa  domin kaddamar da yakin neman zaben sa. 

Ya kara da cewa, a yayin ziyarar, zai kaddamar da dukkan ofisoshi da rassan jam’iyyar a Yobe ta Arewa domin su fara gudanar da ayyukansu na yakin neman zaben jam’iyyar a dukkan matakai.

“Dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankoso zai ziyarci Damaturu da Potiskum nan gaba,” in ji shi. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: