Ciwon Ciki Zai Hana Ronaldo Haskawa a Wasan Sada Zumuncin Najeriya da Portugal

Daga BBC Hausa

Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo ba zai haska a wasan sada zumuncin shirye-shiryen gasar cin kofin duniya da za a fafata tsakanin Najeriya da kasarsa a wannan Alhamis ɗin ba.

A cewar kocinsa Fernando Santos, ɗan wasan tun jiya bai fito atisaye ba, kuma yana bukatar hutu na ɗan wani lokaci.

A wannan makon ne Ronaldo mai shekara 37 ya caccaki kungiyar Manchester United a wata hira da aka yi da shi, inda ya ke nuna cewa ba ya darajar kocinsa, Erik ten Hag saboda abubuwan da yake yi masa.

Sannan ya nuna cewa United ba ta yi masa adalci ba, kuma akwai ‘yan wasan da ba sa farin cikin kasancewarsa a kungiyar.

Idan Ronaldo ya warke ana sa rai ya haska a karo na biyar a gasar cin kofin duniya, babu mamaki kuma ta karshe ga ɗan wasan.

Portugal za ta yi fafatawar farko ne da Ghana a ranar 24 ga watan Nuwamba, kafin daga bisani su haɗu da Uruguay da kuma Koriya Ta Kudu.

Ɗan wasan da kasarsa Portugal ba su taɓa lashe kofin duniya ba, amma sun taka rawar gani a gasar cin kofin Turai ta 2016 da kuma lashe League a 2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: