Ce-ce-ku-ce Kan Cancantar Shigar Malaman Addini Siyasa


Daga BBC Hausa


Batun shigar malaman addinin Musulunci siyasa ya kwana biyu yana jawo ce-ce-ku-ce tsakanin ‘yan Najeriya.

A zaɓukan da aka yi na baya a ƙasar, an ji yadda malamai daban-daban suka fito suka bayyana ra’ayoyinsu kan wasu ‘yan takarar siyasa, lamarin da ake ganin ya jawo rashin jituwa tsakanin wasu ɓangarorin.

Ya danganta da fahimtar da kowa yake yi wa malaman addini kan ra’ayinsu na siyasa.

Wasu na yi musu fahimta cewa suna lallashin mabiyansu don su zaɓi mutumin kirki da ziummar a samu ci gaba mai ɗorewa a ƙasa.

Wasu kuma na ganin cewa akwai malaman da suna yi ne domin ra’ayin ƙashin kansu, watakila domin biyan wata buƙata tasu ko ta ƙungiyarsu.

Wasu malaman kan yi hannunka mai sanda a wajen wa’azi domin jawo ra’ayin jama’a kan wanda za a zaɓa, wasu kuma kan fito ɓaro-ɓaro su kama sunan ɗan siyasa a cikin masallaci ko kuma a wurin wa’azi domin nema masa ƙuri’a.

Ganin cewa an kaɗa gangar siyasar 2023 a Najeriya, tuni wasu malaman suka soma kama sunayen wasu ‘ƴan takara da kiran a zabe su.

Dangane da wannan batu, BBC ta tuntuɓi wasu malaman Musulunci da kuma nazarin fatawowin da wasu malaman suka bayar dangane da ra’ayin siyasa.

Bisa nazarin da BBC ta yi, malaman sun kasu gida uku, wasu na goyon bayan malamai su shiga siyasa, wasu kuma ba sa goyon baya, inda wasu kuma suka ce sun tsaya a tsakiya.

Malaman da ke goyon bayan malaman addini su shiga siyasa.

Sheikh Kabiru GombeBE
Cikin wani bidiyon wa’azi da ƙungiyar Izala ta wallafa a shafinta na Facebook, an ga sakataren kungiyar Sheikh Kabiru Haruna Gombe yana bayyana cewa a baya sun yi kira ga ‘ƴan Izala da su fito su yi zaɓe inda ya ce suna fata nan gaba ma idan suka ƙara kira za su fito su yi zaɓen.

A lokacin da yake kan mambarin wa’azin, Sheikh Kabiru ya ce “duk wanda a shirye yake idan gobe shugabanmu na ƙungiya na ƙasa Sheikh Bala Lau ya ce ga umarni ku je ku zaɓi wane, zai yi biyayya zai amsa kamar yadda ya yi, ya ɗaga hannu ya ce Allahu Akbar”.

Bayan ya kammala waɗannan kalaman sai jama’a suka yi kabbara da ƙarfi domin nuna goyon bayansu.

Bayan haka, Kabiru Gombe ya yi rantsuwa da Allah cewa ba za su zaɓi ɗan siyasa don ya ba su duniya ba.

Haka kuma Sheikh Kabirun ya fito ya yi tsinuwa ga duk wanda yake da labarin cewa Buhari ya taɓa ba su kuɗi amma ya rufa musu asiri bai faɗa ba.

Sheikh Musa Yusuf Asadus SunnahADU
BBC ta tuntuɓi Sheikh Musa Yusuf Asadus Sunnah domin jin ra’ayinsa kan batun malamai su shiga siyasa, inda ya ce shi ma yana goyon bayan malamai su shiga siyasa amma da sharuɗɗa.

Ya bayyana cewa idan Malaman addinin Musulunci ba su shiga siyasa ba ai na sauran addinai za su shiga, inda ya ce babu dalilin da zai sa sauran su shiga su kuma ba za su shiga ba.

“Ni ina da ra’ayin malamai su shiga siyasa su kuma sa baki a cikin harkar siyasa, amma da ma’auni biyu. Ma’auni na farko na ilimi; ma’auni na biyu kuma adalci,” in ji Sheikh Musa.

“Ma’auni na farkon, idan za su saka baki ta fuskar ilimi to duk wani abu da za su saka baki a harkar siyasa ko wani mutum a matsayinsa na ɗan siyasa, kada su zo su yi magana a kansa haka nan ba su da cikakken ilimi a kansa.

“Ma’auni na biyu kuma shi ne ma’auni na adalci. Tun da su malaman addini ne su kalli wanda ya yi daidai ko ba sa jam’iyyar da yake kai su tabbatar da daidai ya yi, wanda ya yi kuskure ko yana jam’iyyarsu su tabbatar da abin da ya yi ba daidai ba ne, kuskure ya yi, domin su wakilan addini ne.”

Malaman da suka tsaya a tsakiya
Sheikh Muhammad Nuru Khalid (Digital Imam
A wata hira da BBC ta yi da shi, Sheikh Nuru Khalid ya bayyana cewa ba ya ganin laifin malaman da suka shiga siyasa, haka kuma ba ya ganin laifin waɗanda suka ƙi shiga.

Ya bayyana cewa malaman da suka shiga siyasa suna da ra’ayin sai an shiga abu kafin a gyara shi, malam ya ce hakan “batu ne na gaskiya domin mutum ba zai iya gyara abu ba idan bai matse shi ba”.

Haka kuma Sheikh Nuru ya ce malaman da suka ƙi shiga siyasa sun yi haka ne “saboda sun ga akasarin waɗanda suka shiga a baya narkewa suka yi, yana mai cewa cikin malamai 10 da za su shiga ɗaya ne kawai ke tsira bai narke ba”.

Malam ya bayyana cewa wasu malaman gudun kada su narke ɗin ne suka ƙi shiga siyasar.


“Abin da ya sa nake tsakiya shi ne, duk wanda ya shiga da niyyar gyara, idan lamarin ya buwaye shi bai iya gyarawa ba, idan narkewar tasa ba ta shafi imaninsa ba, to za a yi masa uzuri saboda kasancewar abin ya fi ƙarfinsa. Wanda kuma ya tsaya ya ƙi shiga domin gudun kada ya narke shi ma bai yi laifi ba.”

Malaman da ba sa goyon bayan malamai su shiga siyasa.

Sheikh Ibrahim Ahmad Maqari
Sheikh Ibrahim Maqari na daga cikin malaman da kwatakwata ba sa goyon bayan malamai su shiga fagen siyasa ko kuma su sa baki.

A wata fatawa da malamin ya bayar wadda aka naɗa a bidiyo, ya bayyana cewa ya kamata a raba tsakanin siyasa da da’awa, yana cewa “ɗan siyasa daban malamin addini daban”.

“Idan malamin addini yana so ya sa baki a siyasa ya cire hular addini ya koma honarabul ya yi magana cikin siyasa. Idan ba haka ba to mambarinsa haƙƙin Allah ne, mambarinsa wakilcin Allah da Manzon Allah yake yi, kada ya yaudari al’umma,” in ji Sheikh Maqari.

Sheikh Maqari ya kuma bayyana cewa “duk mutumin da ya ƙara zuwa zai tallata muku wani to ku ba shi sharaɗi; ya ɗauki Al-Kur’ani ya rantse ba a ba shi ko kobo a duhu ba, ya karɓi Al-Kur’ani ya rantse ba kwangila ya karɓo ba, ya rantse da Allah wanda ya halicce shi babu wanda ya biya shi wannan abin da yake yi”.

A cewarsa: “Idan zai iya wannan rantsuwar, wato abin da ya yi imani da shi ne yake kiran ku zuwa gare shi, to Allah ya ba da sa’a.

Amma kada ku ci gaba da bari ana yaudarar ku, ana amfani da wani sauti da kuke ji, ana kwasar ku ana cinikin ku ana sayar wa ‘ƴan siyasa da ku kuma alhalin kuɗin nan shi da ƴaƴansa zai je ya amfana.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: