Buhari Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Hukumar Kula Da Aikin ‘Yan Sanda
Daga Wakilinmu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da tsohon Sifeton ‘yan sandan ƙasar Solomon Arase mai ritaya a matsayin sabon shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta ƙasar.
Sabon shugaban ya sha rantsuwar kama aiki ne ranar Laraba a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, gabanin fara taron majalisar zartarwa ta ƙasar.
Watanni biyu da suka gabata ne dai majalisar dattawan ƙasar ta amince da shi a matsayin shugaban hukumar.
Solomon Arase wanda ya yi ritaya daga aikin ɗan sanda a shekarar 2016, ya yi aiki a sassa daban-daban na rundunar ‘yan sandan ƙasar, kafin daga bisani ya zama babban sifeton ‘yan sandan ƙasar a shekarar 2015.