Borno : Shugaban CAN Ya Yabawa Tinubu Wajen Zabar Kashim Shettima A Matsayin Mataimakinsa

Daga Sani Gazas Chinade, Maiduguri 

Shugaban kungiyar mabiya addinin Kirista ta Nijeriya (CAN), reshen jihar Borno, Bishop Mohammed Naga, ya yaba wa dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Sanata Asiwaju Bola Ahmed Tinubu dangane da zabar Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a zaben 2023 mai zuwa.

Bishop Naga, ya bayyana goyon bayan kungiyar Kiristocin jihar Borno ranar Litinin a sanarwar manema labaru mai dauke da da hannun sa, tare da bayyana cewa al’ummar Kirista a jihar Borno sun sakata da walawa a lokacin da Sanata Shettima ya yi mulkin jihar tsakanin 2011 zuwa 2019; fiye da kowane lokaci.

Mr Naga ya bayyana cewa, “Yan uwana, musamman wadanda ba ‘yan asalin jihar Borno bane, ba zasu fahimci zancen ba, amma ni da kai mun fi kowa sanin hakan. Wanda a tarihin jihar Borno, ba a taba samun Gwamnan da ya yi wa al’ummar Kirista adalci kamar Gwamna Kashim Shettima ba. 

Haka nan ina jaddadawa karara a gaban  Allah Mahalicina (tsakani da Allah) kuma wannan ita ce gaskiya tsagwaronta daya daga ciki shi ne a lokacin sa ne aka samu adadi mai yawa na Kiristoci sun tafi aikin Ibada tun a 2011.”

“Har wala yau, ina fadar hakan ne ba domin tsoro ko neman yabon wani ba, ko domin nine shugaban qungiyar CAN ba, kuma babu sisin-kwabo da na nake karba daga aljihun gwamnati ko wata ma’aikata ba, face kawai gaskiya ce nake fada Kuma bisa dalilan irin halin ya kamata da yake nuna wa mabiya addinin Kiristanci a nan Borno.”

“A yanzu haka akwai wasu  daga misalan kyautatawarsa garemu, a lokacin da Boko Haram suka farmaki al’ummar Gwoza tare da kaurowa zuwa Maiduguri ga wasun su inda Gwamna da kansa ya zo cibiyarmu ta CAN Centre dake nan Jerusalem ward har sau biyu a watanin June da July a 2014.

Yayin da ya bai wa yan gudun hijirarmu tallafin Naira milyan 10. Sannan a karshen watan October 2014, yan gudun hijirar Gwoza sun karu zuwa mutum 42,000, inda Gwamna Shettima ya qara dawowa tare da bayar da karin tallafin Naira miliyan 10. Kuma ya taimaka wa Kiristocin jihar Borno da suka yi qaura zuwa Kamaru tallafin naira miliyan 5 domin su dawo gida.”

“Haka zalika kuma, ya bayar da karin wasu kudade kimanin Naira miliyan 5 ga wasu Kiristocin da ba ‘yan jihar Borno bane wadanda ke zaman hijira a Kamaru domin su dawo Nijeriya.” 

“Sannan kuma, Gwamna Kashim ya bai wa hukumar SEMA ta Borno umurnin bai wa Kiristoci kayan abinci ta hanyar shugabanin kungiyar CAN. 

Haka kuma, a wancan lokacin, Gwamna Kashim ya yi tsayin daka cewa Kiristoci da Musulmi ‘yan gudun hijira su zauna sansani daya, wanda daga bisani mu ka bukaci a rabasu, saboda gudun kar wata hatsaniya ta biyo baya tsakani.”

“A bangare guda, bisa hakikanin gaskiya, a matsayinmu na Kiristoci kuma masu wa’azi, ba mu da wani shakku dangane da matakin da Asiwaju ya dauka na zabar Musulmi ya yi masa mataimaki, saboda a zahiri ba shi da wata matsala kuma muna farin-ciki kan wannan mataki kashi.” Ta bakin shugaban CAN reshen Jihar Borno.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: