Ban Taba Sayen Komai Ba A Takarata Ta Sanatan Kano Ta Kudu – Hon Kawu Sumaila

Daga Ibrahim Hamisu

Dan takarar Sanatan Kano ta Kudu a Jam’iyyar NNPP Hon. Sulaiman  Abdurahman Kawu Sumaila (OFR) ya bayyana cewa shi yaron mutanen Kano ta Kudu ne kuma yaron mutanen jihar Kano ne, inda ya ce su ne suka tsaya masa har ya ke take Sanatan Kano ta kudu.

Hon. Kawu ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da kungiyoyi suke kai masa a gidansa da Kano.

Dan takarar Sanatan ya ce “Mu a siyasarmu abinda ke damun alummarmu shi ne za mu je mu yi masu, kuma alummarmu birni da kyauye sun gama shiryawa ranar zabe kawai su ke jira”.

Ya kara da cewa ” tun da na fara takara Sanatan  Kano ta kudu ban taba buga Poster  ko banner da kudi na ba, ya zuwa yanzu Muna da motoci fiye da guda 150 da mutane suka ba mu, kawai mutane sunce waraka suke nema Kuma mun hadu da yan Amana zaa tabbatar da waraka a Nigeriya da izinin Allah”. inji Hon. Abdurahman Kawu Sumaila.

Ziyarar dai ta samu halartar kungiyoyin al’ummomi karamar hukumar kiru da Gaya da  Bunkure da Kuma karamar hukumar birnin  Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: