Babu Wanda Ya Isa Ya Dakatar Da Ni Daga PDP – Nyesom Wike


Daga Mujtaba Gali


Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ƙalubalanci jam’iyyarsa ta PDP kan barazanar korarsa, yana mai cewa babu wanda ya isa.


A lokacin wata tattaunawa da ya yi da kafar Talabijin Channels, ministan ya ce, ba ya tsoron kowa kuma abin da ya ke yi babu batun saɓa ƙa’idar jam’iyya ko kuma zagon-ƙasa.


Wike wanda tsohon gwamnan Ribas ne, ya ce shi dai a iya saninsa bai ga wani shugaba a PDP da ya ke da ikon iya korarsa ba, ko yi masa barazana.


Ministan ya kuma jadadda cewa shi shugaba Tinubu ya ke yiwa aiki, ba wai APC ba don haka babu wanda ya ke bin sa bashi ko ya wajaba ya nemi afuwa daga gareshi.


Sabon ministan na Abuja ya kuma shaida cewa nan da watanni takwas za a ga canji sosai a birni, saboda jirgin ƙasan da zai ke yawo a cikin gari zai soma aiki, sannan mulkinsa zai dawo da abubuwa sosai musamman ainihin tsarin Abuja.


Yana mai shaida cewa dama masu arzikin Abuja ke karya dokoki birnin, don haka za su ɗau duk wani mataki na laɗabtarwa da tabbatar da cewa doka ta yi aiki a kan kowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: