Ba Zan Yi Wa Sabon Gwamnan Kano Katsalandan Ba – Kwankwaso


Daga Mujtaba Gali

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen da ya wuce a Najeriya, Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba zai yi wa gwamnan Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, katsalandan cikin harkokin mulkinsa ba.

Kwankwaso, wanda shi ne jagoran NNPP na ƙasa, kuma wanda ake gani a matsayin ubangidan Abba Gida-Gida a siyasance, ya ce idan gwamnan mai jiran gado ya nemi shawararsa, zai ba shi.

Wasu mutane sun yi ta nuna fargabar cewa ba lallai ne Abba Kabir Yusuf ya samu cikakken ikon tafiyar da gwamnatin Kano ba, idan an rantsar da shi, saboda mai yiwuwa Kwankwaso zai yi ta ba shi umarni da yi masa katsalandan.

Sai dai, yaayin wata hira da BBC, tsohon gwamnan na Kano, ya ce a matsayinsa na ɗan Kano zai riƙa ankarar da gwamnatin wadda za a rantsar a ƙarshen watan Mayu, duk lokacin da ya ga ta kauce hanya.

Ya ce “Ai shi mulki ko mai shararka ne, ka ba shi, to ka koma waje ɗaya in ya nemi shawararka ka bayar, idan kuwa bai nema ba, sai ka yi shiru.”
abin da ya sani, in ji Kwankwaso, shi ne a lokacin da yake gwamna a Kano, da su Abba aka yi mulkin, su ne suka taimaka ya cimma nasarar da ya samu.

Kwankwaso ya ce, “ A yanzu na tabbata shirmen da Ganduje ya yi a Kano, ai Abba ya wuce wannan.

Saboda haka ne ma, muka zauna muka duba dukkan mutanen namu muka ɗauki wanda muke ganin idan Allah ya yarda in dai irin matsaloli na Ganduje ne ba za a samu ba.”

Tsohon gwamnan, ya ce,” Dukkanninmu a jihar Kano muna farin ciki Allah ya fitar da su, kuma muna addu’ar Allah ya raka taki gona.”

A cewar Kwankwaso, abin da yake so a sani shi ne ”ko wane ne yake mulkin Kano, ko soja ko ma wane ne, to ba za mu kyale shi, ya yi rashin kyautawa ba.”

“Don haka ko Abba ne ke mulki ko ma waye duk wani abu da yake daidai za mu faɗa masa, idan ma ba daidai ba ne za mu faɗa.”

Kwankwaso ya ce, shi abin da ya sani, shi ne za a gyara duk wasu abubuwa da aka yi ba daidai ba, a lokacin gwamnati mai barin gado.

Ya kuma ce, za su yi hakan ne don a gyara Kano ta yi kyau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: