Ba Wani Rashin Jituwa Tsakanina Da Buhari – Tinubu

Daga Mujtaba Gali

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce babu wani saɓani tsakaninsa da Shugaba Buhari, yana cewa har yanzu mai biyayya ne shi ga shugaban.

Ɗan takarar ya bayyana haka ne ga magoya bayansa lokacin da ke yakin neman zaɓe a Gusau babban birnin Jihar Zamfara, lokacin da ya yi musu alƙawarin zai kawo ƙarshen matsalolin da suka addabi Jihar, tare da bunƙasa harkokin noma.

Kalaman da ɗan takarar ya yi game da sauyin kuɗi da kuma layin man fetur da ake fama da shi a faɗin ƙasar.

Tuni aka riƙa ce-ce-ku–ce game da maganganun nasa ana ganin kamar wani saɓani ne ya faru tsakaninsa da shugaba Buhari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: