ASUU : Yajin Aiki ya Sa Ka Daliban Najeriya Karatu a kasashen waje

Daga BBC Hausa

A ‘yan watannin da suka wuce, Isiyaku Abubakar ya yi shirin fara sabuwar rayuwa a matsayin dalilbi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, bayan ya ci jarrabawar share fagen shiga jami’a ta JAMB. Babu abin da yake kallo illa fara karatu a daya daga cikin jami’o’in Najeriya.

To amma tun da aka fara yajin aikin kungiyar malam jami’a ta ASUU a watan Fabrairun 2022 da har yanzu ake ciki, Isiyaku ya tafi Uganda, inda yake karatu da jami’ar kasa da kasa da ke Gabashin Afrika.

”Ban taba sha’awar karatu a waje ba sai don yajin aikin ASUU, na yi jiran su dawo, amma hakan ba ta samu ba shi ya sa na yanke shawara zuwa Uganda.”

‘’Matsalar ASUU ta sa kusan na ce abu ne da ba zai yiwuwa ba ka gama karatunka cikin lokaci. Alal misali, a kwas din shekara hudu mutum na iya shekara shida ko bakwai, shi ya sa dalibai da dama ke daukar matakin zuwa wasu kasashen domin yin digiri,” in ji Isyaku.

Ya kara da cewa ”na samu ‘yan Najeriya da dama a makarantar da nake, kuma su ma rikicin ASUU ne ya sa suka je Uganda karatu.”Yusufu Abdulhadi yana aji biyu ne a Jami’ar Bayero, kuma shi ma ya ce yajin aikin da ya ki ci ya ki cinyewa ne ya sa ya dauki matakin barin Najeriya zuwa jami’ar Les Cours Sonou da ke Jamhuriyar Benin.

Dalibai da dama kamar Isiyaku da Yusuf sun yanke shawara cewa neman ilimi a wata kasa shi ne abu mafi a’ala a gare su saboda gaza samun shi a kasashensu a halin da ake ciki.

Sai dai akwai wadanda ke son tsallakawa kasashen wajen kamar Isiyaku da Yusuf amma ba su da kudi yin hakan.

Gwamnatin Buhari ta gurfanar da ASUU a kotu12 Satumba 2022 Saboda haka ba su da zabi illa su cigaba da jira har ranar da ASUU za ta janye yajin aiki.

Ameerah Abdullahi na da cikinsu, kuma a cewarta da a ce iyayenta na da hali, da tuni ta yi watsi da kwas din Chemistry da take karantawa a Jami’ar Tarayya da ke Dutse tun watannin baya.

‘’Da yanzu ina aji uku, amma har yanzu aji daya nake saboda kullen korona yanzu kuma ga yajin aikin ASUU, na rantse rashin kudi ya sa har yanzu nake Najeriya”.

Kasuwar masu sana’ar kai dalibai kasashen waje ta bude

Mahmud Bashir na da kamfanin da ke kai dalibai kasashen waje a Kano da ke arewacin Najeriya.

Ya fada wa BBC cewa a ‘yan watannin da suka wuce ya taimaka wa dalibai akalla 30 da ke karatu a jami’o’in tarayya samun gurabu a jami’o’in kasashen waje.

Ya ce da dama na zuwa Togo, Benin da kuma Uganda saboda saukin kudi, idan aka kwatanta da zuwa kasashen Turai.

‘’Ina iya tabbatar maka da cewa a ‘yan watannin da suka wuce saboda yajin aiki, na taimaki dalibai 30 sun samu gurbin karatu a kasashe daban-daban a wajen Najeriya.”

‘’A yanzu kasashen da ‘yan Najeriya suka fi zuwa su ne Benin, Togo, Ghana da Uganda,” in ji Mahmud.

Ya kara da cewa ”na san wanda yake aji hudu a Najeriya, amma saboda jami’ar da yake sun bata masa lokaci wurin ba shi takardun shaidar kwasa-kwasan da ya yi don ya cigaba a wata jami’ar, ya yi watsi da komai ya faro daga aji daya a Jamhuriyar Benin.

Abdul Danladi ,shi ma wani mai kamfanin samar wa dalibai gurbin karatu ne a kasashen waje a jihar Kano, kuma ya ce kasuwancinsa ya bunkasa saboda yajin aikin ASUU.

Ya ce a cikin wata biyu ya samar wa dalibai 10 guraben karatu a kasashen waje.

‘’Dalibai 10 a cikin wata biyu na taimaka. Na goman ma kwanan nan ya kira ni yake fada min cewa har ya fara shiga aji a jami’ar Gabashin Afrika da ke Uganda.”

‘’Maza da mata duka suna so su fita waje karatu, kuma ina ganin takaicin abin da ke faruwa ne ya sa suke ta neman mafita,” in ji Abdul.

Wani ma’aikacin jami’ar Bayero da ke Kano da bai yadda mu ambaci sunansa ba, ya tabbatar mana da cewa ana samun karuwar bukatar karbar takardar shaidar kwasa-kwasai daga dalibai a ‘yan watannin da suka wuce.

A cewarsa suna yi musu abin da suka bukata don suna da hakkin zabar inda suke so su yi karatu.Daya daga cikin abubuwan da ake ja-in-ja kan su tsakanin ASUU da gwamnatin Najeriya shi ne tsarin da za a rika biyansu a kansa.

ASUU ta kafe cewa sai gwamnati ta yi amfani da tsarin UTAS don biyansu albashi.

A cewar Shugaban ASUU Victor Emmanuel Osodoke, hukumar habaka fasahar zamani ta NITDA da ya kamata ta binciki yadda UTAS din ke aiki ta ki gudanar da aikinta, duk da kwaskwarimar da aka yi wa tsarin.

A yan watannin da suka wuce gwamnatin Najeriya ta yi ta zama da ASUU don warware dambarwar. A 2009 ne gwamnati ta aminta za ta yi bita kan bukatar malaman jami’ar duk bayan shekara biyar.

Daga cikin akwai batun albashinsu, da kuma tsarin da ake biyansu a kan shi.

To amma Shugaban hukumar ta NITDA, Kashifu Inuwa na fada wa manema labarai cewa tsarin UTAS da ASUU ke kai ya gaza tsallake gwajin da suka yi masa.

Akan haka hukumar ta bukaci ASUU ta je ta yi masa UTAS din gyare-gyare ta sake dawowa da shi.

Fafatawa tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya

Yanzu haka gwamnatin Najeriya ta shigar da ASUU kara.

Gwamnatin na bukatar kotun ma’aikatan ta umarci malaman da su dawo janye yajin aikin da suke yi.

Sai dai bayan zamanta na farko, kotun ta dage zaman har zuwa ranar 16 ga watan Satumba da mu ke ciki.

A wasikar da ya aike wa magatakardan kotun, Ministan Kwadago da samar da Ayyukan yi, Dr Chris Ngige ya bukaci kotun da ta gaggauta hukunci kan lamarin don a kawo karshe dambarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: