ASUU : Ta Tsawaita Yajin Aikin Jami’o’i da Mako 12


Daga BBC Hausa

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU ta tsawaita yajin aikinta da mako 12 daga ranar Litinin 9 ga watan Mayun 2022.

Shugaban ƙungiyar Emmanuel Asodeke ne ya sanar da tsawaita yajin aikin a wata sanarwa da ASUU ɗin ta fitar, wanda ya ce an ɗauki matakin ne bayan da Kwamitin Zartarwa ya yi wani taron gaggawa a sakatariyar ƙungiyar da ke Jami’ar Abuja.

Mista Asodeke ya ce bayan tattaunawa sosai da gwamnati kan kawo ƙarshen yajin aikin zuwa yanzu ta gano cewa gwamnati ta ƙi ɗaukar haƙƙoƙin da suka ratayu a wuyanta kan batutuwan da ƙungiyar ta bujiro da su a shekarar 2020.

“Hakan ne ya sa muka sake tsawaita yajin aikin da mako 12 domin bai wa gwamnati lokaci don warware matsalolin da suke a ƙasa,” in ji shi.

Ya kuma ƙara da cewa ASUU ba ta ji daɗin yadda kwamitin da gwamnatin tarayya ta naɗa don warware matsalar ya nuna halin ko in kula kan batun ba, ta yadda ko sau ɗaya ba su kira su don ganawa ba.

Za mu ci gaba da kawo muku duk wani ƙarin bayani da muka samu kan wannan labari a nan gaba. Sai ku ci gaba da bibiyar shafin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: