Ankarrama shugaban hukumar tattara haraji ta jihar Gombe da lambar yabo

Daga Ukasha Ibrahim, Gombe

Gammayar kungiyar daliban Arewacin Najeriya (National Association Of Northern Nigeria Students (NANNS) sun karrama shugaban hukumar tattara haraji ta jihar Abubakar Inuwa Tata bisa jajircewarsa akan gudanar da aiki a hukumar tattara haraji ta jihar Gombe.

Gamayyar daliban sun samu tarba daga wajen manyan shuwagabbanin hukumar ta tattara haraji ta jiha, Abubakar Inuwa Tata, manyan darektoci da kuma shuwagabbanin bangaren daban-dabam na hukumar, 

Bayan bude taro da addu’a, shugaban gamayyar kungiyar daliban Arewacin Najeriya ya bayyana Abubakar Inuwa Tata a matsayin mutun mai gaskiya kuma jajirtacce akan Aikinsa,

“Hakika kana daya daga cikin mutanen da wannan gamayyara kungiya ta zaba yayin gudanar da zamanta na mussaman da takeyi a kowane farkon shekara, ta zabeka bisa jajircewarka wajen gani ka dakile cin hanci da rashawa dakuma kokarinka wajen samar da daidaito da inganta ma`iakatan hukumar”. in ji shugaban kungiyar.

Shugaban Daliban ya kara da ambaton Tata a matsayin hazikin ma’aikacin daya samar da cigaba a jihar Gombe dakuma aiki bisa kwarewa da hazaka.

Ya kuma bayyana Abubakar Inuwa Tata a jerin mutum na uku cikin wadanda suka samu irin wannan lambar girmamawa a Arewacin Najeriya bayan MarigayiYusuf Maitama Sule (Dan masanin Kano) dakuma Hon. D Ghana. 

A nasa jawabinsa shugaban tattara kudin harajin jihar Gombe, Abubakar Inuwa Tata ya bayyana godiyarsa bisa wannan karammawa da shuwagabannin gammayar kungiyar daliban Arewacin Nijeriya suka karramashi da ita. 

Ya kara da cewa:-“Naji matukar farin ciki ganin yadda naganku matasa kuma masu kokari wajen nuna kishi da kula da lamarin Al’umma, wannan lambar yabo ba iyatawa bace da ma’aikatan hukumar tattara haraji ne dakuma daukacin al’ummar Jihar Gombe baki daya” 

Abubakar Inuwa Tata kara dacewa yanzu zai kara daura daraman yaki da cin hanci da rashawa dakuma kara jajircewa wajen ganin Jihar ta amfana da hukumar ta tattara harajin jihar wajen kawo ayyukan cigaba mai dorewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: