Ana Ci Gaba da Daukar Sabon Fim Din ‘Madugu’

Daga Ibrahim Hamisu

Shahararren Kamfanin use shirya Finafinan nan mai su na Sultan Film Factory, ya yunkuro inda yanzu haka ya ke shirya wani gawurtaccen Fim mai dogon zango mai suna MADUGU.

Fim din wanda ake daukarsa a cikin birnin Kano, zaa shafe kwana 15 ana daukar aikinsa.

Daraktan Fim din kuma jarumi a cikin Fim din,  Sultan Abdurrazak ya bayyana cewa Kamfanin Sultan ya dade yana shirya Finafinan Hausa amma bai taba yin Fim da zai kayatar irin wannan ba.

Ya kuma ce ” Fim din Madugu ya dauko wani muhimman Sakonni  da al’umma suke fama da shi a wannan lokaci shiyasa muka dauko muka gina labarin da shi”.

“Mafi yawan idan zaa yi Fim a yanzu akan je hotal ne ayi ya fi komai sauki saboda wahalar da Fim din rayuwar Talakawa ya ke da shi, wannan fim na Magudu ya dauko rayuwar talakawa ta can kasa-kasa inda ya nuna hakikanin yadda ta ke, don haka Ina tabbatar maka da cewa irin wannan Fim din ba su da yawa a masana’atar Kannywood” A cewar Sultan Abdurrazak.

Kazalika, ya yi wa masu kallo albishir da cewa nan da wata daya mai zuwa ake sa ran fara haska shi a tashar Arewa 24, sannan a haska a tashoshin YouTube.

Ita ma jarumar Fim din Khadija Muhammad wacce ta fito a matsayin Sadiya ta bayyana cewa ” gaskiya Fim din Madugu na musamman ne domin  idan aka yi laakari da irin  ma’aikata da kyan aikin da ake amfani da su tabbas Ina ganin Fim din zai amfanar a kasa da ma duniya baki daya”.

Abba B. Ismail da aka sani da Kabugawa shi ne mashiryin shirin kuma mai kula da cigaban shirin, ya bayyana cewa ” wannan mai suna ‘Madugu’ Yana magana akan abin da ke faruwa a cikin alummarmu ya Sosawa al’umma abinda ke yi masu kaika yi, ba na jin wannan shiri, don lallai Ina kira ga al’umma da zarar Fim din nan ya fito a kalle shi Ina da yakini zai kawo gyara a cikin al’umma”.

Fim din ya kunshi Jarumai kamarsu Shuaibu Lawan Kumurchi, Aisha Humaira, Yahanasu Sani, Lawan Ahmad da sauran manyan Jarumai Maza da Mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: