An shawarci Hukumar NDLEA da ta rinka kai samame ma’aikatun gwamnati domin ana samun masu fakewa tare da ta’ammalli da miyagun kwayoyi

Daga Wakilinmu

Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato (Grassroot Care and Aid Foundation), Amb. Auwal Muhd Danlarabawa yayi kira akan shugabanni da hukumar yaƙi da sha da fatauci da miyagun kwayoyi da su kawo ɗauki wuraren da ake shaye-shaye kamar sakatariyar ƙananan hukumomi da ofisoshin gwamnati jihar da sauran wuraren taruwar ƴan siyasa dan magance ta’ammali da kayan maye.

Ɗanlarabawa yace da yawa ana kokawa da yadda matasa ke amfani ma’aikatun Gwamnati da wuraren da ake hada-hadar siyasa tare da fakewa ana shaye-shaye wanda ba mai hanawa ballantana saka doka ta hana su ci gaba da aikata laifuka.

Amb Auwal Muhd Danlarabawa ya ƙara da cewa masu kawo korafi sun bayyana cewa idan aka je sakatariyar da ake da su a kananan hukumomi za a tarar da dandazon matasa wadanda ke ta’ammali da kayan maye da shaye-shaye da kuma ma’aikatun gwamnati da sauran wuraren da ake gudanar da harkokin siyasa da wasu ma’aikatu na gwamnati.

Shin abin tambaya anan shine hukumar da ke yaki da shaye- shaye bata san da waɗannan wuraren ba ne, ko an cire su daga jerin wuraren da ba’a kama masu shaye- shaye a wurin an basu lasisin ci gaba da aikata laifukan ta’ammali da miyagun kwayoyi da tabar wiwi da sauransu ?

Daga Amb. Danlarabawa yayi kira ga al’umma da wannan hukuma da ta samar da wani tsari wanda zai hana yin amfani da wurare da za’a taru don yin shaye- shaye a kowacce unguwa, kamar ramuka, kangwaye, gidajen Kallo, cinema, gidan gala gidan Dambe, da sauransu, hakan zai taimaka sosai wajen dakilewa da Kuma hana yawaitar matasa masu shaye-shaye a unguwanni da ma gari baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: