An Sasanta RIkicin Sarautar Hausawa A Lagos

Daga BBC Hausa

Ana ci gaba da mayar da martani tun bayan sasanta tsakanin al’ummar Hausawa da Fulani da rikicin shugabanci ya dabaibaye a jihar Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci yunƙurin sasantawar kafin daga bisani ya tabbatar da sarautar Sarkin Hausawan Legas da ta Sarkin Fulanin Lagos, bisa la’akari da fahimtar asali da tushe.

Ana ganin matakin ya kawo ƙarshen taƙaddamar da aka shafe shekaru ana yi, amma ɓangarorin da ke jayayya kan sarautun guda biyu, ba su ce uffan ba.

Kwamitin kawo daidaito na jihar Legas ya tabbatar da Alhaji Aminu Yaro Dogara a matsayin sarkin Hausawa da Alhaji Abubakar Muhammadu Bambado a matsayin sarkin Fulanin jihar Legas.

Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Legas da gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya yi la’akari da tushen sarautun biyu.

Wannan dai a cewar kwamitin ya kawo ƙarshen taƙaddamar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa tsakanin Alhaji Aminu Yaro Dogara da Alhaji Garba Kabiru da kowanne ke ikirari cewa shi ne Sarkin Hausawan jihar Legas.

Zaman wanda kwamitin kawo daidaito karkashin jihar Legas da aka yi dai ya kawo karshen rikicin shugabancin al’ummar Hausawa da ta shafe shekaru wanda ya raba hankalin al’ummar Hausawa biyu.Alhami Aminu Yaro Dogara ya bayyana yadda ya ji da wannan lamari da a yanzu aka tabbatar masa da wannan sarauta, inda ya ce gaskiya ce ta yi halinta.

Ya kuma ce a shirye yake ya tabbatar da an samu hadin kai ga daukacin al’ummar arewaci domin su cimma bukatar da ta kai su Legas da kuma damawa da su kan harkokin siyasa da muƙamai a a cikin gwamnati. 

Shi ma dai Sarkin Fulani Muhammadu Banbado wannan kwamiti ya sahale masa a matsayin Sarkin Fulanin jihar Legas – ya tofa albarkacin bakinsa, yana mai cewa burinsu a yanzu shi ne haɗa kan al’ummar arewacin kasar mazauna jihar Legas.

Tushen rikicin

Marigayi Sani Kabiru Sani ya yi ikirarin cewa shi ne sarkin Hausawa, alhali Alhaji Yaro Dogara, shi ne ke kan wannan kujera kuma shi ne ya naɗa marigayi Sani Kabiru a matsayin Sarkin Hausawan unguwar Ebute Metta a Legas. 

Taƙaddamar ta kusan shekara 40 ta raba kawunan al’ummar arewa mazauna jihar tare nuna adawa tsakanin mabiya shugabannin biyu.Bayan rasuwar sarkin Hausawa Alhaji Yaro Dogara a shekara ta 2007 ne aka naɗa ɗansa, Alhaji Muhammd Aminu Yaro Dogara a matsayin sabon Sarkin Hausawa na jihar Legas, to sai dai zuri’ar Sani Kabiru ta ci gaba da ikirari cewa suke jagorantar al’ummar Hausawan jihar.

Kawo wannan lokaci dai ɓangaren Alhaji Garba Kabiru bai ce uffan ba, to amma wata takarda da ake dangantawa da bangaren Alhaji Garba Kabiru ta nuna rashin jin dadinta da matsayar da ake a yanzu.

Wani bincike mai zaman kansa da al’ummar arewacin Naijeriya mazauna jihar Legas suka yi shekara goma sha daya baya, sun yi ikirari cewa akwai Hausawa da sauran ‘yan arewacin Naijeriya mazauna Legas akalla miliyan uku.

Gwamnatin jihar Legas dai ba ta boye muhinmancin al’ummar arewacin kasar musanman a lokutan da suke neman gudunmowarsu kamar a lokutan zabe da sauran muhinman al’amura cikin jihar. Wanda a yanzu gudunmowarsu ta kai ana damawa da su cikin al’amuran jihar da bayar da mukamanti da na siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: