An Sake Gano Gawar Mutum Biyar a Kebbi

Daga Mujtaba Gali

An gano ƙarin gawar mutum biyar da suka rasu a hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi ranar Talata, inda masu aikin ceto ke ci gaba da lalubo sauran.

Jirgin ruwan ya kife a garin Samanaji na Karamar Hukumar Koko-Bese lokacin da yake ɗauke da fasinjoji fiye da 100, amma an samu nasarar ceto mafi yawa daga cikinsu.

Alhaji Yahaya Bello Koko, wanda shi ne shugaban Karamar Hukumar Koko-Besi, ya tabbatar wa BBC cewa hadarin ya faru ne lokacin da mutanen ke komawa gida daga gona.

Ya ce mutane sun cika jirgin maƙil tare da mata da kuma yara, abin da ya sa ya rabe biyu a tsakiyar ruwa kasancewar tsohon jirgi ne.

Shugaban karamar hukumar ya ƙara da cewa an ceto mutum fiye da 80, inda aka gano gawa 10 a ranar Laraba.

Zuwa yanzu an gano jimillar gawa 15 kenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: