An Nada Buni Matsayin Sarautar Taremobowei A Delta

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

A kokarin da ya ke da shi na hada kan kasa masarautar Gbaramatu da ke Jihar Delta a Kudancin Najeriya ta baiwa Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni  sarautar Taremobowei na Masarautar ta Gbaramatu. 

An bayyana Gwamna Buni Tamfar kadarko na hada kan kasa  da kuma samar da hadin kan al’umma.

Masarautar ta Gbaramatu ta ce ta gamsu da irin nasarorin da ya samu a matsayinsa na Gwamnan Jiha, mai bin tafarkin dimokaradiyya kuma jekadan ci gaba a kasar nan.

Taken shi ne ya zaburar da Gwamna Buni don kara himma wajen inganta hadin kan kasa domin dunkulewar Nijeriya baki daya.

Babban Daraktan Hulda da Yada Labarai da manema Labarai naa gwamna, Mamman Mohammed ne ya sanar da nadin Gwamnan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: