An Mayar Da Ƴan Najeriya 144 Da Suka Maƙale A Nijar


Daga Mujtaba Gali

Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, ta ce ta karɓi ƙarin rukuni na ƴan Najeriya 144 waɗanda suka maƙale a Jamhuriyar Niger.


Kodinetan hukumar a jihar Kano, Nuraddeen Abdullahi, shi ya bayyana hakan yayin da yake karɓar mutanen a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano. Mutanen sun iso gida ne da misalin karfe 2:30 na rana.


Ya ce an mayar da mutanen ne karkashin wani shiri na Hukumar Kula da Ƴan Cirani ta Duniya daga Niamey, babban birnin ƙasar.
Mutanen sun haɗa da maza 106 da mata 16 da kuma yara 22.


Mista Abdullahi ya ce mutanen da aka dawo da su ɗin sun fito ne daga sassan ƙasar da dama – wasu daga Kano da Kaduna da Katsina da Abia da Sokoto da Edo – da sauransu.


A cewarsa, za a horar da mutanen kan sana’o’i daban-daban tare da ba su jari domin dogaro da kansu.


Kodinetan ya shawarci ƴan Najeriya da su daina saka rayukansu cikin haɗari ta hanyar tafiye-tafiye da nufin samun ingantaccen rayuwa a wasu ƙasashe, inda ya ce ba ƙasar da tafi Najeriya.


Kamfanin Dillanicin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa tsakanin watan Febrairu da Maris, an an dawo da ƴan Najeriya 300 zuwa gida waɗanda suka maƙale a Nijer.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: