An Kaddamar Gangamin Kan Bullar Cutar Kyanda A Yobe

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnatin Jihar Yobe da hadin kan al’ummar jihar Yobe tare da hadin gwiwar hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar za su kaddamar da gangami wayar da kan jama’a game da barkewar cutar kyanda a jihar.

Shugabar kwamitin na Jiha Hajiya Husna Ibrahim a cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a Damaturu, ta bukaci masu ruwa da tsaki su dauki matakin gaggawa dangane da kokarin shawo kan wannan annoba ta kyanda.

Hajiya Husna ta yi kira ga daukacin masu ruwa da tsakin da ke cikin al’umma da suka hada kai da ma’aikatan lafiya don ganin su sanya hannu a kan dakile bullar wannan annoba cikin lokaci.

Ta kuma koka da yadda aka samu rahoton bullar cutar, inda ta kara da cewa gwamnati na daukar matakai cikin gaggawa wajen tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya mai sauki ga daukacin ‘yan jihar.

“Ko da yake cutar tana da alaƙa da yanayin da ake ciki a yanzu amma ana iya kokari don ganin magance ta.”

Ta ce tunin Kwamitin ya gudanar da taron tsare-tsare don samar da tsarin ayyuka a kan hakan.

Wannan taro dai an gudanar da shi ne a ofishin EOC ya kuma samar da muhimman sakonni don wayar da kan jama’a kan rigakafin cutar kyanda a cikin jihar ta Yobe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: