An Halaka Mayakan ISWAP A Harin Da Rundunar MNJTF Suka Yi A Tafkin Chadi

Daga Sani Gazas Chinade, Maiduguri

Kwararren masanin harkokin tsaro nan a Arewa maso Gabas na yankin tafkin Chadi Zagazola Makama ya ruwalto daga shafin sadarwa sa na yanar gizo na Zagazola cewa, jiragen yaki na rundunar hadin gwiwa ta MNJTF sun halaka mayakan kungiyar ISWAP da ke yammacin Afirka da daman gaske tare da jikkata wasu da dama.

Rahotan na Zagazola ya tabbatar da cewar, an kashe ‘yan ta’addan ne a ranar Juma’a, 1 ga watan Yuni, sakamakon ci gaba da ruwan bama-bamai da jiragen sojoji suka yi, a Sabon Tumbun da Jibularam, a karamar hukumar Marte a Arewa maso Gabashin Jihar Borno wadda sai yanzu ne rahoton ya bayyana. 

Majiyar leken asiri ta shaidawa Zagazola cewa hare-haren da jiragen suka kai wa ‘yan ta’addan da dama ne jim kadan bayan kammala sallar Juma’a a Sansanin su. 

Majiyoyin sun ce an aiwatar da wannan hari ne  bisa sahihan rahotannin sirri da ke nuni da cewa’yan  kungiyar ta ISWAP, na haduwa da yawa.

“Rahoton na nuna cewar lalle wadannan hare-hare da jiragen yakin na rundunar tsaron ta MNJTF suka rika kaiwa mayakan na ISWA ya yi  tasiri matuka kasancewar mayakan Jihadi da dama suka mutu, wasu kuma suka samu munanan raunuka.

“Ba za mu iya tantance ainihin adadin ‘yan ta’addan da aka kashe ba, amma sun fi dozin,” in ji shi.

Rundunar ta MNJTF ta zafafa kai hare-hare ta hadin gwiwa domin kakkabe yankin Tumbuns gaba daya daga ayyukan ‘yan ta’adda a karkashin Operation Lake Sanity, reshen Operation HADIN KAI.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: