An Fara Horar Da ‘Yan Bijilantai 600 Dabarun Tunkarar ‘Yan Bindiga A Katsina

Daga Abbas A. Dangida

An kaddamar da shirin horar da jami’an bijilantai 600 dabarun tunkarar ‘yan bindiga gaba da gaba a jihar Katsina.

An kaddamar da fara shirin bayar da horo ga jami’an sintiri har su dari shida da suka fito daga ƙananan hukumomi 34 dake fadin jihar.

An kaddamar da fara basu horon ne a sansanin horar da jami’an Sibil difense dake nan cikin birnin Katsina a yau Laraba.

Mai taimaka wa Gwamnan jihar Katsina a kan sha’anin tsaro Alhaji Ibrahim Katsina, ya ce an dakko mutum dari shidan ne a duk fadin jihar Katsina kuma maza da mata da suka aminta da samun horon da kashin kansu.

Ya ce tun da farko an fara ba :yan bijilantai 500 irin wannan horon, yanzun kuma 600 sun shiga, nan gaba kuma za a kara jami’ai 1900 da za su sami irin wannan horon.

Ibrahim Katsina ya ce za a basu horon tunkarar ‘yan bindiga ba sai sun shigo cikin garuruwa ba, kuma za a basu horon koyon sarrafa makaman zamani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: