An Bukaci Al`umma Da Su Yawaita Aikata Kyawawan Ayyuka Cikin Watan Zul-Hajj

Daga Muazu Hardawa a  Birnin Madina

Sallar juma’a ta farko a cikin watan Zul-Hajj ta gudana a birnin Madina da ke kasar Saudiyya inda limamin masallaci na biyu a duniya wato masallacin Manzo S.A.W da ke Madina ya gabatar da hudubar ta wannan ranar 2 ga Zul Hajj 1443 hijiriyya daidai da 1/7/2022 Miladiyya Hudubar tsawon minti 30 limamin ya yi ta game da muhimmancin aikin Hajji da Umrah da kuma yin jihàdi Fisabilillahi don daukaka kalmar Allah.

Don haka yace dukkan nasara na daga wajen Ubangiji Allah, don haka ya bukaci jama’a su tsarkake zukatan su, su aikata ayyuka na gari da yawan ambaton Allah.

Kuma mutane su kyautatawa juna su nisanci tada fitina a tsakanin juna, su bi umarnin Allah zuwa masallatansa masu tsarki don bauta da yin sallah da ambaton Allah wanda ke arzuta mutane ba tare da sanin su ba.

Bayan haka hudubar ta umarci mutane su rika kiyaye harsunan su tare da fadin gaskiya a kuma nisanci cutar da juna a kyautata wa musakai da masu karamin karfi a bi maganar Allah a bada zakka a kyautata masu a kuma nisanci cutar da juna.

Hudubar masallacin ta Madina ta hori mutane su aikata ayyuka na kwarai cikin wannan wata da ake ibadar aikin Hajji daya daga cikin shika shikan musulunci. Don haka kada Alhaji yayi fasikanci ko jidali ko tashin hankali kamar yadda yazo cikin Alkur’ani mai girma, Manzo SAW ya yi umarni cikin ayoyi da Hadisai, don haka ya jaddada muhimmancin ayyukan alheri musamman a wannan wata na Zul Hajj  wacce za a hau Arfah  ranar juma’a mai zuwa In Sha Allah.

Huduba ta biyu ta fara da godewa Allah da Salati ga Manzo SAW ya nemi mutane su godewa Allah su bi umarni Manzo SAW wajen bautawa Allah madaukakin Sarki tare da aiki na kwarai da bin umarnin Manzo SAW.

Daga nan hudubar ta ci gaba da magana kan muhimmancin aikin Hajji da yin sallah cikin jam’i da nasihohi masu yawa don mutane su samu dacewa a karbi ayyukan su don  samun Rahamar Ubangiji Allah madaukakin Sarki.

Kuma ya jaddada muhimmancin azumin ranar arfa da tsayuwar ranar arfa inda daga karshe yayi addu’o’i masu yawa da kuma rokon Allah ya karbi ayyukan mahajjata da kuma nemawa bayin Allah gafara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: