Al’ummar Kano, a bi doka da oda – Jakada Usman

Daga Wakilinmu

An yi kira ga al’ummar jihar Kano da su ci gaba da bin doka da oda tare da yin biyayya ga gwamnatin jihar Kano a kar­kashin gwamna Dakta Abdul­lahi Umar Ganduje, matukar al’umma na kiyaye doka da oda gwamnatin za ta ji dadin gudanar da aikace-aikace ga al’umma.

Bayanin ya fito daga bakin babban Kwamandan samar da tsaro na farin kaya PEACE CORPS na jihar Kano Amba­sada Usman Abubakar Aliyu, a lokacin da yake zanatawa da manema labarai ciki har da Albishir.

Jakadan zaman lafiya ya yi anfani da wannan dama da jinjina wa al’ummar jihar, a kan yadda suka kiyaye doka da oda musamman a lokacin da aka hana fita sakamakon annobar Korona. Wani abu kuma da gwamnatin ta yi lo­kacin kullen shi ne rarraba kayan tallafin abinci kyauta ga al’ummar jihar wanda har yanzu ana ci gaba da bayarwa musamman ga mabukata.

Ya ce shi ma a lokacin kullen zaman gidan ya yi ba­kin kokarinsa wajen rarraba kayan abinci da kuma sinada­rin wanke hannu ga wadansu al’ummomin da ke jihar da gidajen Rediyo.

Bayan wannan in ji Kwa­mandan zaman lafiya, ya ce su kan taimaka wa wadansu daga cikin makarantun da ke jihar saboda haka suna aiki tare da bayar da gudunmawa daidai gwargwado wajen ci gaban al’ummar jihar musamman a kan harkar samar da tsaro, sai ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da ba su hadin kai da goyon baya wajen ganin tsaro sun inganta a jihar da kasa baki daya.

Daga karshe ya jawo han­kulan al’ummar arewacin ka­sar musamman matasa maza da mata da su kara ta shi tsaye wajen neman ilimi, domin yawancin abin da yake faruwa na rashin tsaro, rashin ilimi na daya daga cikin abin da ke haifar da shi, matukar akwai ilimi ga al’umma musamman matasa ba za su yarda a rinka amfani da su wajen tayar da hankalin al’umma ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: