Alhazai Sun Gudanar Da Juma`a A Filin Arfa

Daga Muazu Hardawa a filin Arfa

Alhazan Nijeriya sama da dubu 40 da suka ziyarci kasa mai tsarki sun bi takwarorinsu na duniya inda suka gudanar da sallar azahar da la’asar lokaci guda a daidai lokacin da kuma musulmi da ba sa filin Arfa don aikin Hajji ke yin azumi da sallar juma`ah a garuruwansu.

Sheikh Mohammed Kabir Adam daya daga cikin limaman babban masallacin juma`ah na Abuja na cikin wanda suka jagoranci sallar ta azahar da la’asar a wani tantin Ahazan Nijeriya a filin arfa inda bayan gabatar da sallah ta azhar da la’asar a hade yayi nasiha da jan hankali game da muhimmancin wannan rana ta arfa a duniya, kasancewarta rana mafi girma da alheri a musulunci.

Cikin nasiharsa ya  bukaci Alhazan.da suka zo sauke farali a bana sun godewa Allah saboda an zabo su daga cikin.mutane milyan 200, suka shiga cikin kimanin mutane dubu arba’in da suka zo don wannan aiki na Hajji a Saudiyya wanda daya ne daga shika shikan musulunci.

Sheikh Mohammed Kabir ya bukaci Alhazan su yiwa kansu da iyalansu da kasa baki daya addu`ah don samun ingancin tsaro da walwala da saukin kayan more, don.mutane su dawo cikin hayyacin su.

Shi ma shugaban hukumar jin dadin Alhazai ta kasa, Alhaji Zakirullah Kulle Hassan ya kai rangadi shemomin alhazan a filin arfa inda ya gode musu tare da yaba halin alhazan Nijeriya game da hakuri da suka yi musamman a wasu jihohi saboda matsalolin da aka samu na jinkirin tashi zuwa kasa mai tsarki.

Ya bayyana cewa kowane Alhaji za a maida shi cikin aminci kamar yadda aka dauko shi. Yace idan an fara jigilar Alhazan za a maida su wanda suka fara zuwa sune na farko kafin.wanda suka biyo su kuma sai su bi bayan su har a.maida kowa gidansa.

Nan.da goshin magariba.kuma Alhazan za su hau motoci zuwa filin Muzdalifa inda za su kwana daga nan kuma sai su dauki tsakuwar jifan shaidan su je su jefi jamrah daga nan su wuce Makka don yin dawafin dakin Allah da sa’ayi kafin su sake dawowa Minna su jira ranakun jifa ta biyu da ta uku da sauran ibadun da suka rage irin su yanka hadaya da aski da makamantan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: