Aikin Jigilar Alhazan Nijeriya Na Gudana Cikin Nasara.. Ibrahim Mahmood
Daga Muazu Hardawa a Madina
Hukumar jin dadin Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta bayyana samun nasarar gudanar da aikin jigilar Alhazanta zuwa kasar Saudiyya kamar yadda aka tsara.
Wakilinmu a Madina ya tattauna da jagoran hukumar ta NAHCON, Alhaji Ibrahim Idris Mahmood inda ya bayyana sakonsa ga mahajjata da suka iso kasa mai tsarki da wanda ke kan hanya. su kasance masu da’a da biyayya da kuma tuna kasarmu game da halin da take ciki don haka ya bukaci kowa ya yi add`ua don Allah Ya kawo mana dauki.
Ya kuma bukaci alhazan da su kasance masu bin dokoki da yin biyayya ga shugabanni don samun gudanar da ayyukan su cikin nasara, ya bukaci Alhazan na bana su yiwa Allah godiya da ya kira su a daidai lolacin da kasar Saudiyya ta dakatar da zuwa aikin Hajji shekaru biyu. Inda a bana suka amince a zo aikin hajji a wani yanayi da aka takaita yawan Alhazai daga Nijeriya zuwa mutane dubu 43 daga cikin kusan mutane dubu dari da ke zuwa a baya.
Don haka ya bukaci wanda ba su samu zuwa a bana ba su yi hakuri su jira badi In Sha Allah su tanadi kudin su don zuwa sauke farali cikin yardar Allah.
Alhaji Ibrahim Idris ya kara da cewa hukumar jin dadin Alhazai ta kasa NAHCON ta yi dukkan tanadin da ya dace don inganta rayuwar.mahajjata ta yadda za su ji dadin sauke farali.
An tanadi kwamitoci da dama da suka hada da na karbar Alhazai a filin jirgi har zuwa masaukai da kwamitin lura da lafiyar Alhazai da na yada labarai da na samar da abinci da ya dace da lafiyar alhazai. Yace har kwamitin lura da lafiya da muhalli da kuma wa’:azi don ganin Alhazai sun gudanar da ayykansu cikin nasara da kwanciyar hankali duk an tanada kuma kowa na aikinsa yadda ya dace.
Yace sama da Alhazai dubu goma sun bar Madina zuwa Makka yayin da saura kuma suna isowa Madina daga Nijeriya cikin kwanciyar hankali da tsari, ya bayyana cewa da yardar Allah za a gama jigilar alhazan cikin lokacin da aka tsara kuma za a mayar da kowa gida lafiya a lokacin da aka tsara.