Abba Kabir Yusuf Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kano

Daga Mujtaba Gali

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.

Abba Kabir, wanda ake yi wa da laƙabi da Abba Gida-gida ya samu nasara ne a kan abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC mai mulki Nasiru Yusuf Gawuna.

Gawuna shi ne mataimakin gwmnan jihar Kano.

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan Kano Farfesa Dikko Ahmad Ibrahim ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri’u 890,70

Sakamakon ya nuna cewa jam’iyyar PDP ce ta zo ta uku, inda Sadik Wali ya samu ƙuri’u 15,957, sai kuma Sha’aban Ibrahim Sharaɗa na jam’iyyar ADP ya samu ƙuri’u 9,402.

A shekarar 2019 ne Abba Kabir ya fara takarar gwamnan kano inda ya yi takara da Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC.

Jam’iyyar NNPP ce ta lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, ta kuma lashe biyu cikin uku na kujerun sanatocin Kano, sannan da mafi yawancin kujerun majalisar wakilai dag jihar ta Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: