A Najeriya Ambaliyar Ruwa Ta Shafi Sama Da Mutum 500,000

Daga BBC Hausa

Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya, NEMA, ta ce sama da mutum dubu ɗari biyar ne ambaliyar ruwa ta shafa a ƙasar.

Shugaban Hukumar ta NEMA a Najeriya Dr Mustapha Habib Ahmad ne ya shaida wa BBC hakan a Kano, inda ya ce suna fargabar cewar za a kuma samu ƙaruwar adadin, kasancewar akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa a ƙarin wasu jihohin sakamakon ruwan da aka sako daga madatsar ruwa ta Lardu da ke jamhuriyar Kamaru.

Dr Mustapha ya ce yawan ruwa da ake da shi ya sa dukkan jihohi da ƙauyukan da ke kusa da kogin Neja da na Benue na cikin haɗari. Ya ce hasashen da hukuma ta fitar game da ambaliyar ruwa a bana, an ga jihohi 32 da ambaliyar ruwan za ta shafa kuma “mun tura wa duka ƙananan hukumomi”.

“Mun bai wa jihohi shawara da su kafa kwamitin gaggawa saboda aikin dole daga ƙasa za a fara ba daga sama ba – da an yi tsari mai kyau, da an kaucewa ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi, a cewarsa.

https://8d4dc0f31fb016de65f1ef5e65e9a5b1.safeframe.googlesyndication.com/safeframe/1-0-38/html/container.html A cewarsa, batun sauyin yanayi yana taka rawa wajen sauye-sauyen da ake samu game da saukar ruwan sama.

 Ya bayyana cewa a bana, ruwa ya ci gaba da sauka har watan da muke ciki na Satumba saɓanin yadda aka gani bara da ruwan sama ya ja baya da wuri.

Dr Mustapha ya ce babban hadarin da Najeriya ke ciki a yanzu shi ne sako ruwa daga madatsar ruwa Lardu a Jamhuriyar Kamaru – “idan aka saki madatsar ruwa ta Lardu, ambaliyar ruwan za ta sake shafar wasu jihohi guda 11 waɗanda suke bakin kogin Neja da Benue.

Batun Agaji…

A cewar Dr Mustapha hukumarsu ta yi tanadi sosai domin taimaka wa mutanen da ibtila’in ya shafa. Sai dai ya ce kamata ya yi ƙananan hukumomi su fara kai ɗauki ta hanyar kwashe mutane su mayar da su wajen da babu barazanar ambaliyar ruwan.

Ya ce zuwa yanzu, an kai kayayyakin agaji zuwa wasu kananan hukumomi na jihar Jigawa, “akwai tawaga a jihar Neja, sun kai kaya.”

Da yake magana kan asarar da manoma suka tafka kuwa, Dr Mustapha ya bayyana cewa “a 2018 da 2020, Shugaban Ƙasa ya kafa wani kwamiti aka ba da taimako ga mutanen, wannan aikin ba aikin NEMA bane, sia shugaban ƙasa ya ba da izini .”

Ya ce suna buƙatar bayanan manoman da ambaliyar ruwan ta shafa saboda za su yi amfani da ƙididdiga ne domin tabbatar da adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: