2020: JIHAR JIGAWA DA FITATTUN MUTANEN DA SUKA RASU.


Daga Mansur Ahmed Jahun


Jihar Jigawa ta gamu da abubuwa na rashin daɗi, zulumi, jimami, fargaba, faɗuwar gaba, firgici, da alhini na faruwar abubuwa da dama wadda na tabbata jihar ba za ta taɓa mantawa da wannan shekarar ba musamman da ta zama sanadin rasuwar manyan mutane da suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jihar wasu aka dama dasu tun kafin samun ƴancin jihar, wasu sun sake fito da sunan jihar a idon duniya kama daga ma’aikatan gwamnati, ƴan siyasa, yana kasuwa, masu riƙe da sarauta da sauran al’umma.

Shekarar 2020, a jihar Jigawa za’a iya cewa ta shafi kowa kai tsaye ko ta wata fuska da ta shuka masa wani ciwo, alhini, ko firgicin da ba zai manta dashi ba.

Ɗauke uzurin Covid-19 da ta shafi dukkan duniya kuma ta taɓawa kowa uzurinsa ta tsayar da agogon duniya a tsaye chak.

Ita ce shekarar da aka rasa Rt. Hon. Adamu Ahmed Sarawa, tsohon shugaban majalisar dokokin jiha, Farfesa Haruna Wakili, tsohon kwamishinan Ilmi kuma mataimakin shugaban jami’ar Bayero, Rt. Hon. Ilyasu Sa’idu Dunduɓus tsohon shugaban majalisar jihar Jigawa, Hon. Yahaya Muhammad Bigman tsohon ɗan majalisar dokoki mai wakiltar Sule Tankarkar, Hon. Adamu Fagen Gawo tsohon ɗan majalisar Garki da Ɓaɓura, Hon. Aminu Sidi Ƴalleman, tsohon kwamishinan jihar Jigawa, Alhaji Yusuf Alassan, Barman Gumel, Alhaji Haruna Idris Magama.

Khadi Muhammad Inuwa Ali, tsohon Grand Khadi na jiha, Alhaji Sabo Ɗangƴatum, Hon. Aƙilu Liman Auyakayi tsohon shugaban ƙaramar hukumar Auyo, Hon. Babangida Milo Hadejia, Dr. Abdulƙadir Isa Dutse tsohon shugaban asibitin Mallam Aminu Kano,

Alhaji Abubakar Abdullahi Sarkin Gabas Dutse/Daya daga cikin masu zaben Sarki kuma Hakimin Shuwarin, Alh Lawan Gwaram, Ɗan Darman/Dan majalissar Sarki, Alhaji Ali Maitama Gwaram (Sarkin Shanun Dutse/Dan majalissar Sarki, Alhaji Saleh Chiroma (Sarkin Fada Dutse/Dan majalissar Sarki, Alhaji Bashir Aujara, Sarkin Yamma Dutse/ Hakimin Chamo

Alhaji Sabo Muhammed, Galadiman Gumel, Mukaddashin babban Dan majalissar Sarki, Alh Jibo Muhammed, Dan majalissar Mai wakilta kungiyar ‘yan kasuwa, Alhaji Ayuba Muhammed Sarkin Kudu, Hakimin Meɗu, Alhaji Yusuf Alhassan, Barman Gumel, Alhaji Sani Ibrahim Magajin Garin Gumel Hakimim Gumel Kudu, Alhaji Idris Muhammed, Matawallen Gumel Dan majalissar Sarki, Alhaji Lawan Garba Falakin Gumel, Malam Ibrahim Albasu, Talban Gumel Malam Musa Adamu, Uban Doman Gumel.

Maji daɗin Hadejia, Ɗan Malikin Hadejia Hakimin Waje, Haruna Idris Magama Kogunan Hdejia, Alhaji Isma’il Ibrahim, Jarman Ringim, Eng. Kamilu Umar Matawallen Ringim, Sanata Garba S. Taura, Sarkin Yaƙin Ringim da sauransu da dama.

Jihar tayi fama da sace – sace da asarar rayuka saboda sata daga ɓarayi, anyi garkuwa da al’umma da dama wasu an same su wasu sun rasa rayukansu sanadin haka, jihar tayi asarar rayuka da yawa sanadin hatsarin mota. Al’ummomi da dama a jihar nan sun rasa iyayensu, yayunsu, surukunsa, abokansu, da danginsu

Muna roƙon Allah kar ya maimaita mana irin wannan shekarar, Allah ya zaunar da jihar mu lafiya ya kawo mana arziƙi mai ɗorewa ya ɗaukaka al’ummarmu su shahara a fannon rayuwa kamar yadda suka shahara a lokacin mulkin Sule Lamido.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: